8 Janairu 2020 - 16:38
Syria Ta Nuna Goyon Bayanta Ga Iran

Kasar Syria Ta Bayyana Cikakken Goyon Bayanta Ga Hakkin Iran Na Kare Kanta daga duk wata barazana

Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti{a.s}ABNA- ta rawaito cewa: Ma’aikatar harkokin wajen kasar Syria ta bayyana  cewa; Hakkin Iran ne ta kare kanta daga hare-hare da kuma duk wata barazanar da Amurka ta ke yi ma ta, ta kuma bukaci Amurka da ta sauya salon yadda ta ke mu’amala da kasashe.

Bayanin ya   ci gaba da cewa; Jamhuriyar Larabawa Ta Syria tana nuna  cikakken goyon bayanta ga al’ummar kasar Iran, akan barazanar da Amurka ta ke yi mata.

Bugu da kari  ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Syria ta dora wa Amurka alhakin dukkanin abinda yake faruwa saboda siyasarta ta ina da yaki da rashin amfani da hankali.